Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne sun kashe wasu matasa biyu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne a kauyen Ogbogboro da ke karamar hukumar Yenagoa a jihar Bayelsa.
Wata majiya mai tushe ta shaida wa Daily trust cewa kisan ba zai rasa nasaba da bambance-bambancen da ke tsakanin kungiyoyin asirin biyu a yankin ba.
Wadanda suka rasun an bayyana sunayensu da Talata Fati mai shekaru 30; da wata Famizibe Clarkson, mai shekaru 25. An kashe su ne a cikin gidajensu da ke unguwar.
Majiyar ta ce yankin na fuskantar hare-hare masu alaka da kungiyoyin asiri da kuma kai hare-hare kan ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba a ‘yan kwanakin nan, yayin da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne ke taruwa a cikin al’umma domin gudanar da ayyukansu.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/jamiyyar-lp-ta-musanta-nadin-charles-okadigbo-a-matsayin-kakakinta/
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, wanda ya tabbatar da kisan, ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike kan lamarin.
Ya ce, “Marigayan da aka bayyana sunayensu a matsayin wata Talata Fati mai shekara 30 da Famizibe Clarkson ‘yar shekara 25 an kashe su a gidansu da ke unguwar Ogbogboro, a Yenagoa a ranar 11 ga Agusta, 2022, da misalin karfe 03:30.
“Bincike na farko ya nuna cewa an kashe mutanen ne a da wani abu da ake zargin na kungiyar asiri ne. An kwashe gawarwakin kuma an ajiye su a dakin ajiye gawarwaki na gwamnatin tarayya domin a tantance gawarwakin.”
DAILY TRUST