‘Yan Arewa Sun Fara jigilar Kayan Abinci Zuwa Nijar Da Kamaru Saboda ƙin biyan kuɗin Diyyar Da Kudu Maso Yamma suka ƙi yi na Naira Bilyan 450 ga ƴan Arewar da aka yi wa ɓarna da kisan gilla a rikicin da ya ɓarke kwanan Baya.
Masu sayar da abinci da dillalan shanu a duk yankin Arewacin kasar nan sun fara karkatar da kayansu da dukkan kayayyakin masarufin da suke sayarwa zuwa kasashen da ke makwabtaka da Jamhuriyar Nijar da Kamaru.
Sun kuma fara toshe hanyoyin kasuwanci zuwa Kudu ta hanyar hana manyan motocin kayan abinci zuwa can kudun.
A ranar Juma’a ne ‘yan arewa suka dakatar da manyan motocin kayayyakin abinci daga yankin arewacin kasar daga shiga jihar Kwara da jihohin da ke makwabtaka da Kudu maso Yamma.
Tun da farko kungiyar Fulani ta nemi a ba ta Naira Bilyan 450 a matsayin diyyar rasa rayukan da suka yi da kuma Asarar Dukiyoyi.