‘Yan bindiga sun far wa fasinjoji, sun kashe guda a Osun

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun far wa wasu matafiya a kan hanyar Osogbo / Ibokun a cikin jihar Osun wanda ya yi sanadiyyar mutuwar fasinja daya.
Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun tare hanya tare da hana ababen hawa motsawa yayin da suke harbi lokaci-lokaci.
An ce sun wa fasinjojin fashin kudinsu da wasu kayayyaki masu muhimmanci sannan suka bar wurin bayan sun harbe daya daga cikin wadanda suka yi garkuwar da su.
An rawaito cewa yan bindigan sun tsere kafin jami’an tsaron da aka tura su Isa wurin.
‘Yan sanda sun kwashe gawar mutumin da aka kashe tare da ceton sauran wadanda abin ya shafa daga wurin.
An ajiye gawar mamacin, wanda ba a iya tantance asalinsa ba, a asibitin jihar da ke Osogbo.