Ƴan bindiga sun fi ƙarfin Jami’an tsaro, suna kashe su kamar Kaji a Zamfara — Inji Mazauna Jahar
Mazauna Jahar Zamfara musamman wanda zaune a karkara, sun bayyana Albashin da ake baiwa Jami’an tsaro da Alawus-Alawus a matsayin Babbar Asara, tunda basu iya shawo kan matsalar tsaro a Jahar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Tunibu ya zabi mataimakinsa a zaben 2023
Da suke jawabi a Babban Birnin Jahar, mutanen Karka sun bayyana baƙin ciki na yadda duk tabbacin da Shuwagabannin Tsaro suka bada akan tsaro, amma sun kasa shawo kan matsalar, domin sun kasa yin bikin Babbar Sallah.
A cewar wani Umar Magami, da yawa daga cikin ƴan ƙauyen sun yi bikin Sallah ɗin su a Gusau da wasu manyan birane, domin babu wani gari a Zamfara da yake da tsaro.
“Duk da tabbacin da Shuwagabannin tsaro suke bada wa, sun yi ne domin gamsar da masu biyan su. Jami’an tsaro ba zasu iya shawo kan matsalar tsaro dake fuskantar Jahar ba.
“Dukkanin Alƙawurran su, sun kasa cikawa kawai ɓaɓatu ne, domin ƴan bindiga suna kashe Jami’an tsaro kamar Kaji.
“Ta yaya za’a samu tsaro alhali ƴan bindiga sune ke rike da garuruwa da dama a Jahar?” Ya yi ƙorafi.