Ƴan Bindiga Sun Hallaka Ƴan Sanda 4, Sun Ƙone Motoci Bayan Sun Tarwatsa Ofishin Ƴan Sanda A Imo
Wasu ƴan bindiga sun kai hari hedikwatar ƴan sanda reshen Agwa da ke karamar hukumar Oguta a jihar Imo, inda suka kashe ƴan sanda hudu.
Ƴan bindigar da suka kai farmaki ofishin ‘yan sandan a daren Juma’a, sun kuma lalata wani bangare na kadarorin sashen da suka haɗa da motoci.
KARANTA WANNAN LABARIN: Manchester United ta yanke shawara kan Sesko
Daga cikin waɗanda harin ya rutsa da su akwai jami’ai biyu maza da mata waɗanda aka ƙona gawarwakinsu.
A cewar wata majiya, ɗaya daga cikin jami’an da aka kashe ya kasance yana da makonni biyu kacal daga fara aiki a Rundunar Ƴan Sanda.
Ɗaya daga cikin motocin da aka kona na jami’in ƴan sandan shiyya ne.
A cikin wannan dare ƴan bindigar sun kuma kai farmaki gidan wani mazaunin unguwar mai suna Ejike, inda suka harbe shi da matarsa kafin su gudu. Ejike ya mutu a nan take.
Wakilin Majiyar mu ya gano cewa ƴan bindigar sun kai harin ne da misalin ƙarfe 10 na dare a cikin wata tifa da wasu motoci guda biyu.
Mazauna yankin sun ce sun fara jin karar harbe-harbe amma suna fargabar fita.
Wata majiyar ƴan sanda ta shaida wa wakilinmu cewa, an zabo wasu ‘yan sanda daga wajen sashin kuma sun mamaye yankin yayin da ake sa ran kwamishinan ƴan sandan jihar, Muhammed Berde na wurin.
Jami’in hulda da jama’a na Rundunar ƴan sandan jihar, CSP Mike Abattam, har yanzu bai ce uffan ba kan lamarin saboda kiran da aka yi masa bai shiga ba.