Ƴan Bindiga Sun Hallaka Ɗaliba zata zana Jarabawar WASSCE a Benue
Ƴan bindiga a ranar Juma’a sun hallaka Ɗalibar Makarantar Sakandare ta St. Monica Girls, Dake Otukpo a Jahar Benue.
Sun hallaka Ɗalibar a lokacin da taje ta cire kayan ta, daga inda ta sanya su, su bushe.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar EFCC Ta Kama ‘Masu Damfara Ta Yanar Gizo 25 A Benue
Ɗalibar tana daga cikin masu rubuta Jarabawar WASSCE da ake gudanar wa a halin yanzu, a lokacin da suka hallaka ta.
“Ɗalibar ta kasance tana karatu a Makarantar Sakandare ta St. Monica Girls dake Otukpo, kuma tana zaune da iyayen ta a lamba ta 38 a hanyar Idikwu.
“Ta wanke kayan ta, ta sanya su bushe, ta fita ta cire kayan ta, a lokacin da ƴan Bindigar suka Harbe ta a kai”, Inji wata Majiya.
Lamarin ya faru a gaban ƙannuwar ta da ake kira da Rosemary, wadda ta ruga domin sanar dashi abinda ya faru.
Ƴan bindigar sun bar gidan bayan sun hallaka ta.
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar SP Catherine Anene ta tabbatar da faruwar lamarin.
Tace “an tabbatar da kisan Ɗalibar. Ya faru ne a ranar Juma’a.