Aƙalla Deliget 3 daga cikin 13 na zaɓen Fidda Gwani na Gwamna a Ƙaramar Hukumar Mariga ta Jahar Niger Ƴan bindiga sun Hallaka Ƴan bindiga.
Majiyar mu ta gano cewa lamarin ya faru ne tsakanin Mariga da Tegina, a yayinda akayi wa mutum 3 kwanton ɓauna a ranar Laraba.
KARANTA WANNAN LABARIN:Da Dumi-Dumi: Gubara Ta Babbake Jarirai 11 A Kasar Senegal
An hallaka su ne akan hanyar su ta komawa Mariga, bayan Jam’iyyar ta ɗage Zaɓen, domin su zo ɗaukar katin shaidar su, biyo bayan zanga-zanga da wasu ƴan takara suka yi da basu amince da sakamakon ba.
A saboda haka, aka umarci Deliget su koma gida tare da ɗauko katin shaidar su, bayan an ɗaga zaɓen zuwa Alhamis.
Waɗanda aka kashen sun haɗa da Mata biyu da Namiji, wanda ba’a sanar da sunayensu ba.
Shugaban Kwamitin Zaɓe kuma Mataimakin Gwamnan Jahar Bayelsa Mr. Lawrence Ewhrudjakpo Wanda Suka bayyana haka a Sakatariyar Jam’iyar Jahar, ya bayyana lamarin a matsayin abun baƙin ciki.
Ewhrudjakpo ya kuma buƙaci Ƴan Takara dasu kawo madadin Deliget wanda suka amince bayan anyi wata taƙaitacciyar tattaunawa.