Ƴan Bindiga Sun Hallaka Makaho da wani Mutum A Kaduna
Wasu ‘yan bindiga sun kashe wasu mutane 2 a kauyen Udawa da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.
Haka zalika, Wasu ‘yan bindiga sun kai wa al’ummar da ke kan titin Kaduna ta Birnin Gwari hari da misalin karfe 8 na daren ranar Lahadi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ka miƙa kanka ga Hukumomin Tsaro – Gwamnatin Rivers ga yaron Atiku
Wani shugaban al’umma, Muhammadu Umaru, wanda ya tabbatar wa Daily Trust kisan gillar a ranar Litinin, ya ce daya daga cikin wadanda aka kashen makaho ne.
Ya ce mazauna yankin sun fito domin faɗa da ƴan bindigar tare da goyon bayan jami’an tsaro da ke kusa da su inda suka tilasta wa ‘yan bindigar tserewa daga cikin al’umma.
“Wadanda aka kashe su ne Sarkin Komo wanda ya shigo kauyen kwanan nan yayin da mutum na biyu makaho ne wanda harsashi ya same shi.
Ya ce matsalar tsaro a yankin na da matukar damuwa, inda ya bukaci hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen kawo karshen kashe-kashen da ake yi a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO) a jihar, DSP Mohammed Jalige, an kasa samun sa a waya, a yayinda aka kira wayar sa bai ɗaga ba, ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
A Wani Labarin kuma: Ka miƙa kanka ga Hukumomin Tsaro – Gwamnatin Rivers ga yaron Atiku
Gwamnatin Jihar Ribas ta shawarci dan majalisa mai Wakiltar mazabar tarayya ta Fatakwal 2, Chinyere Igwe da ya miƙa kansa ga Hukumomin tsaro.
Kiran na zuwa ne kwanaki biyu bayan Gwamna Nyesom Wike ya umarci Hukumomin tsaro a Jihar da su kamo Igwe bisa zargin bin haramtacciyar hanya kan Sana’ar Fetur