Ƴan bindiga sun Hallaka Manoma a Sokoto, sun ɗora Haraji ga wasu
Ƴan bindiga sun hallaka Manoma 11 a Gundumar Ghandi ta Ƙaramar Hukumar Rabah ta Jahar Sokoto.
A cewar bincike, harin ya faru da misalin ƙarfe 12 na rana a ranar Asabar.
Wata majiya tace sun kasance sun aiki a gonakin su, a lokacin da aka kai masu hari.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan Sanda sun ceto wani Mutum da aka sace a ƙauyen Peter Obi
“Sun haɗu dasu a gonakin su, sun hallaka su ba tare da wani dalili ba”, Sakataren Gundumar Ghandi Tukur Muhammad ya shaidawa Jaridar Daily Trust.
Ƴan Bindigar sun yi yunkurin garkuwa dasu amma ƴan sakai suka hana.
Muhammad ya bayyana cewa Manoma 8 an kashe su ne a ƙauyen Kuryar, guda uku kuma a kauyuka dake kusa da wurin.
“Basu son muyi aiki a gona. Suna kai mana hari a kullum. Sun sanya haraji ga wasu kauyuka kafin su girbi amfanin su, kuma wannan shi kaɗai muka dogara a yankin mu”, inji shi.
A lokacin da aka tuntuɓe shi, Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Sokoto DSP Sanusi Abubakar, yace yana kan hanya, amma zai gano abinda ya faru, sannan zai kira daga baya, ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.