Ƴan bindiga sun kai hari kan jami’an Immigration, sun kashe daya, sun jikkata biyu a Jigawa
Wasu ƴan bindiga sun kai hari kan jami’an shige da fice, inda suka kashe daya tare da raunata wasu biyu a karamar hukumar Birniwa ta jihar Jigawa.
Kwanturolan Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa, ACG Ismail Abba Aliyu ne ya bayyana haka a ranar Larabar da ta gabata yayin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar NIS da ke Dutse.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rikicin Atiku-Wike Ba Zai Iya Wargaza PDP Ba – Baraje, Tsohon Shugaban Jam’iyya
Ya ce ‘yan bindigar sun kai hari kan jami’an ne a lokacin da suke sintiri a kan titin Galadi- Birniwa.
A cewarsa, lamarin ya faru ne a ranar Talata, 9 ga watan Agusta, 2022, da misalin karfe 2320 na safe, inda ‘yan bindigar da yawansu ya kai biyar suka isa sansanin ‘yan sintiri a kan babura biyu, suka far wa jami’an.
“Daya na dauke da mutane uku, dayan kuma yana dauke da mutane biyu, nan take suka bude wa jami’an hukumar shige da fice da ke sintiri wuta, lamarin da ya yi sanadin mutuwar daya daga cikin ma’aikatan mai suna Abdullahi Mohammed (CIA) da wasu biyu daga cikin harsashi.
Ya ce jami’an da suka jikkata su ne Abba Musa Kiyawa (DSI) da Zubairu Garba (AII) yayin da wasu jami’ai uku suka tsere daga harin bayan da suka yi da ‘yan bindigar.
Abba ya ce sakamakon musayar wuta da ‘yan bindigar suka yi a cikin daji suka yi watsi da babura da wayar hannu.
Ya ce an mika ma’aikatan biyu da suka jikkata zuwa asibiti domin neman magani.
Kwanturolan ya yi nuni da cewa, babura da wayar hannu da aka kwato za a mika su ga ‘yan sanda domin ci gaba da bincike.
Ya kuma yi kira ga ‘yan kasar da su baiwa jami’an tsaro duk wani bayani mai ma’ana da zai taimaka wajen kamo masu aikata laifuka.