Ƴan bindiga sun kashe mutane 6, sun sace Dagaci a Kano
Ƴan bindiga sun kashe mutane 6 a ƙauyen Karfi na Ƙaramar Hukumar Takai ta Jahar Kano tare da sace Dagacin Ƙauyen Abdulyahya Iko.
Sun kashe su ne a lokacin da suke ƙoƙarin ceto Dagacin Ƙauyen daga hannun ƴan bindigar.
KARANTA WANNAN LABARIN: NAHCON ta tantance Jirage 7 da zasu yi Jigilar Maniyyata Aikin Hajjin 2022
Ƙaramar Hukumar Takai dake Kano ta Kudu ta kasance kilomita 80 daga Birnin Kano, kuma tana maƙwabtaka da ƙauyuka da dama a Jahar Jigawa.
Ƴan bindigar sun shiga ƙauyen a ranar Lahadi da yamma tare da sace Dattijo Mai shekaru 53 Dagacin Ƙauyen.
Sun zo ne a saman Babura guda 3 daga Jahar Bauchi ta hanyar Dajin Ringim a Jahar Jigawa, sannan suna kan hanyar su a lokacin da ƴan ƙauyen suka tattaru domin ceto Dagacin ƙauye.
Ƴan bindigar sun buɗe masu wuta, bayan sun dawo, tare da harbin mutane 9, inda mutane 6 aka tabbatar sun mutu, amma sauran suna Asibiti sun karbar magani.
Dayake tabbatar da lamarin, Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa yace an tura Jami’ai zuwa yankin domin gani an ceto shi, gami da kamo masu aikata laifin.
Comments 1