Ƴan Bindiga sun kashe wani Manomi, sun tafi da Babur
Wasu Ƴan bindiga a ranar Larabar da ta gabata sun bayyana cewa sun kashe wani manomi a unguwar Heipang da ke Ƙaramar Hukumar BarkinLadi a jihar Filato.
An ce Maharan sun kuma yi awon gaba da babur dinsa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Za’a riƙa yiwa Ɗaliban Najeriya Tiyata kyauta
Wata mata mai juna biyu da ke sayar da masara a gefen titi kusa da wurin da lamarin ya faru ta tabbatar wa jaridar PUNCH Metro kisan gilla ranar Alhamis.
Ta ce, “Muna sayar da kayayyakinmu a kan hanya a nan (Heipang) sai kwatsam muka ji karar harbe-harbe.
“Mun tsorata muka gudu. Bayan da muka daga ido muka ga wani mutum yana aiki a gonarsa wanda harbin bindiga ya same shi a kwance a gefen babur dinsa. Sai ga wasu mutane dauke da bindigogi wadanda muka san Fulani ne suka taho wajensa.
“Wasu mutanen kauyen da aka sanar da harbin bindigar, daga baya suka je wurin tare da wasu jami’an tsaro amma ba su sake ganin ‘yan bindigar ba.
“Sun kuma gano cewa ‘yan bindigar sun kuma tafi da babur din manomin da ya rasu.”
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato, Alabo Alfred, ya ce ba a kai rahoton faruwar lamarin ga ofishin sa ba.
PPRO ta ce, “har yanzu ban samu wani rahoto kan lamarin ba. Idan an kai rahoton lamarin ga jami’in ‘yan sanda na yankin, sun fara bincike don kamo wadanda ke da hannu a kisan tare da kwato babur din da ya bata.”