yan bindiga sun mamaye kauyuka 11 sun kashe mutun 15 da jami’in tsaro Daya
Wakilinmu Shu’aibu Ibrahim Gusau
Cikin Daren ranar Alhamis ne wasu kauyuka dake karamar hukumar maradun sun kwana cikin tashin hankali, a yayin da wasu ‘yanbindiga sukayi masu diran mikiya inda suka shiga kauyuka Goma sha daya suka Kuma kashe mutun Goma sha biyar da jami’in tsaro guda daya.
Wata majiya mai tushe daga kauyen Jihiya daya daga cikin al’ummomin da aka mamaye a zantawarsa da kamfanin watsa labarai na (Thunder blowers ) ya ce ‘yan fashin sun kaddamar da harin ne da misalin karfe 5:00 na yamma na ranar Alhamis kan babura suna tashi daga wani kauye zuwa wani.
Cikin kauyukan da suka mamaye akwai Gidan Malam Abu da Shandami da Jeringo da Kuma Dagwarwa sai Jihiya da Daki Hudu da Gidan Runji sai Awala da Akuzo sai Gidan Mudi da Kaura Dole.
A cewar wata majiyar kuma daga Shandame ya ce jimillan wadanda ‘yan fashin suka kashe sunkai mutane goma sha biyar (15) yayin da sukayi awon gaba da shanu da rakuma da tumaki sama da dubu daya.
Ya Kara da cewa sun kone ma’ajiyar hatsi kurmus duk da cewa gidajen zama da shagunan kasuwanci duk sun kone kurmus.
Majiyar tamu ya halarci addu’ar jana’izar wadanda abin ya rutsa da su sannan ya ce jimillar mutane goma sha biyar (15) aka kashe a harin.
Ya fada mana cewa,an kashe mutum (3)a Shandame, sai wasu mutun (4) a Jihiya, sai mutun (2) a Daki Hudu sai mutun (1) a Kaura Dole, an Kuma kashe mata hudu duk matan mutun daya da Kuma wani jami’in ‘Dan sanda a Gidan Runji duk a yayin harin.
Dukkanin kauyukan da aka kaiwa harin suna karkashin Maradun, ‘yan ta’addan sun raunata Babban Limamin masallacin juma’ar na Jihiya kuma yanzu haka yana kwance a asibiti.
Majiyar ta ce, duk da yawan kiraye-kirayen da aka yi yayin harin, jami’an tsaron sun kasa isa inda abin ya faru sai zuwa karfe 8:30 na safiyar Juma’a lokacin da manyan motoci uku (3) na jami’an soja suka isa yankunan da abin ya faru. .
Daga bangaren gwamnatin jihar, Sakataren yada labarai na Gwamna Bello Matawalle Jamilu Iliyasu Birnin Magaji ya ce Gwamnan ya soke ayyukan da yake yi a jihar Sokoto kuma nan da nan ya dawo jihar don jajantawa wadanda harin ‘yan bindiga ya rutsa da su a Maradun da Tsafe.