Masu garkuwa da mutane sun sace Wata Ɗaliba ƴar aji uku dake Nazarin halittar Ɗan Adam a Jami’ar Bayero dake Kano, a lokacin da take tafiya tsakanin Janbulo da Rijiyar Zaki a cikin garin Katsina.
Majiya daga iyayen sun tabbatar wa majiyar jaridar Dimokuraɗiyya inda suka ce, an sace ta ne da misalin ƙarfe 3 na ranar Talata, akan hanyarta, ta komawa gidan a cikin Ɗan sahu.
Masu garkuwa da mutanen sun kuma kira waya a ranar Laraba da safe, inda suka buƙaci a biya su Naira miliyan 100 a matsayin kuɗin fansar ta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da ɗuminsa: Ƙungiyar Ƙwadago, da ƴan gari sun toshe Babbar hanyar Abeokuta zuwa Lagos sabudda rashin kyan hanya
Mai Magana da yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Abdullahi Kiyawa, yace ƴan sanda sun karɓi rahoto da misalin ƙarfe 3 na ranar Talata akan lamarin, kuma sun fara bincike akan lamarin nan take.
Mr Kiyawa yace ana cigaba da ƙoƙari domin gano inda take a halin yanzu.
Mai Magana da Jami’ar Bayero Kano Lamara Azare, yace jami’ar hutun ƙarshen shekara take yi tun watan juli, Kuma zata dawo ne a ranar 1 ga watan Nuwamba.
“Muna hutu. Kuma bamu da wani ɗalibi dake zaune a cikin jami’ar, kuma bamu ji wani lamari akan sace wani ɗalibi,” inji shi.
Comments 1