Ƴan bindiga sun sace mai Juna biyu a Kaduna
Ƴan bindiga sun sace mai ciki a Al’ummar Lema, Mando kusa da Makarantar Horasda Manyan Sojoji ta Zaria, Jahar Kaduna.
Sun sace wasu mutane bakwai a lokacin da ƴan bindiga suka shiga gidaje da misalin ƙarfe 1 na safe a ranar Lahadi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Atiku Da Gwamnonin PDP Sun Taya Adeleke Murnar Nasarar Zaben Osun
Wani daga cikin mazauna yankin, Musa Danladi ya bayyana cewar duk sunji tsoron su fito daga gidan su, saboda harbin bindiga.
“Sun zo ne da misalin ƙarfe 1 na dare, sun tafi da mutane 8 ciki har da mace mai juna biyu a garin. Wannan ba shine lokaci na farko da ƴan bindiga suka kawo hari a ƙauyen”, Inji shi.
Wasu mazauna garin sun yi kira ga Gwamnatin Jahar data kawo masu ɗauki.
Har yanzu Gwamnati bata ce komai ba akan lamarin, amma Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar DSP Mohammed Jalige yace zai bincika ya gano lamarin tare da sanar da abinda ya faru.
Kuma bai fadi komai ba game da lamarin har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.