Kimanin mutane 18, ciki har da mata, aka sace da kashe wani a unguwar Angwar Zalla Udawa a Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jahar Kaduna.
Ƴan bindiga sun zo ƙauyen akan hanyar Kaduna-Birnin Gwari da misalin ƙarfe 12:30 a ranar Lahadi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bikin Sabuwar Shekara: Hatsarin Mota Ya Kashe Mutum 6 A Jihar Ebonyi
Wani shugaban Al’ummar Udawa, Muhammed Umaru wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga Daily Trust, ya bada sunan wanda ya rassun da Bala Jaja.
Yace matar Aure, da matasa da wasu ƙananan yara suna daga cikin wanda aka sacen.
Har yanzu babu wata sanarwa daga Gwamnatin Jaha da Ƴan sanda yayinda duk wani kiran da aka yiwa Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan sanda ta Jahar ASP Jalige Mohammed bai ɗaga ba