Zaman ɗar-ɗar ya ƙaru a Ƙaramar Hukumar Mangu ta Jahar Filato, biyo bayan sace wani mai riƙe da Sarautun gargajiya Diket Gupiya, wanda ƴan ta’adda suka yi.
Gupiya wani Basarake ne Babba a gundumar Pushit, garin Mataimakin Gwamnan Jahar Sonny Tyoden.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dokar Zabe: Ministoci 4 Da Wasu Shugabanni Tilas Su Sauka daga Mukamansu Gabanin 2023
Garkuwa da Gupiya yana zuwa ne watanni biyu bayan sace Charles Mato, Sum Pyem, wani basarake a gundumar Gindiri dake maƙwabta ka dasu, inda suka sake shi daga baya, bayan an biya su kuɗin fansa.
Wasu mazauna garin, wanda suka tabbatar da faruwar lamarin ga Jaridar The PUNCH a Jos a ranar Juma’a, sun bayyana cewa an sace basaraken ne a fadarsa dake Pushit a ranar Alhamis da daddare.
A cewar su, Hakimin yana zaune a Fadarsa yana kallon talabijin da misalin ƙarfe 9 na dare, suka kai masa hari a gidan sa, tare da tafiya dashi wurin da ba’a sani ba har yanzu.
Wani mazaunin garin Philip Moses yace “wannan mummunan lamari ya taɓa mu. Chief Diket Gupiya, Hakimin mu a garin Pushit an sace shi a ranar Alhamis da daddare.”
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Filato Ubah Ogaba ya bayyana cewar, suna sane da sace shi, kuma tuni sun tura wasu jami’an su “domin ceto basaraken.