Ƴan Bindiga sun saki Shugaban Ƙaramar Hukumar Keffi, Jahar Nasarawa
Shugaban Ƙaramar Hukumar Keffi na Jahar Nasarawa Muhammad Shehu-Baba da Mataimakin sa Dr. Tanimu Mohammed sun samu ƴancin kai daga ƴan bindigar da suka kama su.
Mai magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Ramhan Nansel ya tabbatar da haka ga Ƙamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa a ranar Lahadi a Lafia.
KARANTA WANNAN LABARIN: An ƙone Ɗan Fashi da Makami bayan ya ƙwace Motar Manomi a Katsina
Shugaban Ƙaramar Hukumar Keffi da Hadimin sa, an sace su akan hanyar Keffi-Akwanga a ranar Juma’a bayan ƴan bindigar sun sace Ɗan Sandan shi Alhassan Habib.
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar yace sun samu ƴancin kai da misalin ƙarfe 9:00 pm a ranar Asabar, kuma tuni an haɗa su da iyalan su.
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar yace an kama mutane 3 da ake zargi a Al’ummar Gittata na Ƙaramar Hukumar Keffi da suke da hannu a ta’addancin.
“Waɗanda ake zargin da suka fito daga Jahar Kaduna, an kama su a lokacin da suke tattaunawa domin basu kuɗin fansa”, Inji shi.
ASP Nansel yace ƴan sanda basu da masaniya akan biyan wani kuɗin fansa domin sako su.
Ya bayyana cewa masu garkuwa da mutane sun sake su ne a dalilin matsi da Jami’an tsaro suka yi masu.
A wani Labarin kuma, Ɗa Sandan tuni an binne shi kamar yadda musulunci ya tanada a Keffi.
Comments 1