By Abbas Yakubu Yaura
Wasu da ake zargin ‘yan bangar siyasa ne sun kai wa wasu ‘yan jam’iyyar APC hari a Idanre hedikwatar karamar hukumar Idanre ta jihar Ondo tare da raunata su.
Wadanda lamarin ya rutsa da su, wadanda magoya bayan Princess Tosin Ogunlowo ce mai neman takarar yar majalissa an ce suna cikin ayarin motocin ne a lokacin da suke dawowa daga sakatariyar jam’iyyar da ke Akure, babban birnin jihar, a lokacin da ‘yan bindigar suka yi musu kwanton bauna da bindigogi, da guntayen katako, da dai sauran muggan makamai.
A cewar wani ganau, ‘yan barandan sun far wa ‘yan siyasar ne a cikin ayarin motoci guda hudu a kauyen Italorun da ke kan hanyar Idanre zuwa Akure, bayan mai neman takarar ta je bayar da fom din takararta.
“A kan hanyar ne ‘yan barandan suka fito suka far musu da bindigu da kwalabe da fasassun kwalabe inda suka raunata magoya bayanta.
“Sun kuma lalata motocin da ke cikin ayarin. Amma wasu su tsallake rijiya da baya, kuma an garzaya da wadanda suka jikkata asibiti domin yi musu magani,” inji ganau.
Daya daga cikin wadanda harin ya rutsa da su, Gbodi Bamidele, wanda shi ne shugaban majalisar dokokin karamar hukumar Idanre, ya yi zargin cewa harin na daukar nauyi ne, musamman yadda wani dan daba da ya yi kaurin suna a yankin ya jagoranci ‘yan bindigar a yayin harin.
“Lokacin da muka isa Oja Aaye, daya daga cikin ‘yan barandan da ake kira Prof ya zo da wasu suka kawo mana hari.
“Sun zo da bindigogi, kwalaben giya da kayan saran mutane. Mambobinmu sun samu munanan raunuka. An kai su asibiti,” inji shi.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Funmilayo Odunlami, ta tabbatar da faruwar lamarin.
Odunlami ta bayyana cewa fada ne tsakanin magoya bayan wasu ‘yan siyasa biyu a yankin amma ‘yan sanda sun kashe tare da lalata lamarin.
“An samu hatsaniya tsakanin magoya bayan ‘yan takara biyu a yankin, wanda ya kai ga harbin bindiga.
“‘Yan sanda daga Sashen Idanre sun sami damar tabbatar da zaman lafiya yayin da aka kai wadanda abin ya shafa zuwa asibiti,” in ji ta.
Comments 1