Ƴan Daba sun Jikkata Mutane 3 wurin Karɓar Katin Zaɓe a Osun
An tabbatar da jikkata mutane 3 a wasu Al’ummomi na Ƙaramar Hukumar Ilesa ta Yamma ta Jahar Osun a ranar Alhamis, bayan ƴan Daba sun je wuraren da aka tsara domin karɓar Katin Zaɓe, tare da lalata shirin rajistar Katin Zaɓen.
Wannan lamari ya haddasa tsoro a garuruwan Igbogi da Isokun da Ibala gami da cikin Ilesa, wanda hakan ya sanya dole mutane suka zauna cikin gida, a yayinda Ƙaurayen ke cigaba da yin sintiri da manyan makamai.
KARANTA WANNAN LABARIN: NDLEA ta kama mutane 218 masu laifi, ta ƙwace kilogaram 1,471 na Ƙwaya a Imo
Wani mazaunin yankin Ibala, wanda ya buƙaci a sakaye sunan sa yace sunyi hakan ne domin su tsorata mutane daga wuraren karɓar katin zaɓe.
An Kuma gano cewa mutanen da suka raunata, sun samu raunukan ne bayan ƴan Dabar sun yi faɗa tsakanin su.
Da yake jawabi akan lamarin, Mai Magana da Yawun Sibil Difens na Jahar, Olabisi Atanda tace tuni zaman lafiya ya dawo a yankin.
A lokacin da aka tuntuɓi Jami’in Hulɗa da Jama’a na INEC a Osun Seun Osimosu yace har yanzu ba’a daina yin rajistar Katin Zaɓen a wuraren da lamarin ya shafa, amma an ɗauke Ma’aikatan su daga wurin
Comments 1