Ƴan Majalisar Dokoki na jahar Anambra guda 11 daga jami’iyyun PDP, AFGA, sun canja sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.
Waɗanda suka sauya sheƙar sun haɗa da ƴan Majalisar tarayya guda biyar masu ci, da tsofaffi guda huɗu, gami da ƴan Majalisar dokoki guda biyu, inda suka samu tarba daga Shugaban kwamitin ruƙo da tsare-tsaren zaben shugaban jam’iyyar na ƙasa Mai Mala Buni a ranar Alhamis.
Mamman Mohammed, Daraktan ƴan jarida da harkokin kafafen yaɗa labaru na Gwamna Buni, ya bayyana haka ga manema labaru, kamar yadda majiyar jaridar Dimokuraɗiyyar ta ruwaito.
KARANTA WANNAN LABARIN: Legas: Sanwo-Olu Ya Umarci CP Da Ya Nemo Masu Laifi Don Hukunta Su
A jawabin da aka fitar, Gwamna Buni ya taya su murna da suka shigo jam’iyyar, yana mai basu tabbacin cewa, zasu samu dukkanin dama da jindadi dake cikin jam’iyyar.
Masu canja sheƙar, sun shaidawa Gwamna Buni cewa, sun dawo jam’iyyar saboda kyakkyawan shugabanci, daya ciyar da Jami’iyyar a matakin gaba.
Sun sha alwashin kawo dukkanin ƙuri’un mazaɓun su, ga jami’iyyar a zaben Gwamna mai zuwa na Anambra.