Wasu ƴan ta’adda, da ake zargin ƴan ƙungiyar sakai ne a Jahar Sokoto, sun kashe mutane 11, ciki har da limami a ƙauyen Mamande na ƙaramar hukumar Gwadabawa ta jahar Sokoto.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewar an kashe waɗanda lamarin ya shafa, Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewar an kashe waɗanda lamarin ya shafa, a yayinda wasu mutum huɗu da suka jikkata, kuma ƙaramar hukumar ta kaisu Asibiti domin karɓar magani.
Limamin wanda ake kira da suna Malam Aliyu, an ruwaito cewar, yana jan Sallah a wani masallaci a Salame.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sama Da Mutane 50 Sun Mutu Bayan Kifewar Kwale Kwale A Kogin Congo
Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 3:30 na rana a ranar Alhamis.
Haka zalika,
Waɗanda aka kashen, ance sun zone daga inda fulani suke da zama, domin sayen kayayyakin abinci da sauran kayayyaki a kasuwar sati ta Mamande.
Yan ƙungiyar sakan sun yiwa kasuwar ƙawanya daga ƙaramar hukumar Goronyo, tare da farmakar waɗanda suke zargin suna taimakawa ƴan ta’adda.
Ɗan uwan limamin Abdullahi Riskuwa, yace sun kashe ɗan uwansa ne ba tare da laifin komai ba, domin bai taɓa aikata ta’addanci ba.
“Zunubin shi shine ya kasance bafillatani ne.”
Daga cikin waɗanda aka kashe a kasuwar ƴaƴa ne, kuma Ƴan Sakai sun tafi da dabbobin su.
Yayi kira ga Gwamnati data yi ƙwaƙƙwaran bincike akan lamarin, domin ganin an yankema waɗanda suka aikata lamarin hukunci.
Shugaban Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah na jahar, ba’a same shi a waya ba, a yayinda dukkanin layukan sa, suka kasance a rufe.
Haka nan, Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwadabawa Aminu Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace ƴan ƙungiyar sakan ba daga ƙaramar hukumar suke ba.
A lokacin da aka tintiɓe shi, Mai magana da yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar ASP Sanusi Abubakar, yace bai samu labari akan wannan lamari ba, amma yasha alwashin bincikawa tare da sanar da abinda ya faru.
Gwamnan Jahar Aminu Waziru Tambuwal ya dakatar dukkanin aikace-aikacen ƴan sakai a Jahar
Comments 1