Rundunar Ƴan sanda a Jahar Ogun a ranar Litinin, sun kama mutane 18 da ake zargin sun aikata laifuka da dama da suka haɗa da garkuwa da mutane, da fashi da makami, gami da kisa.
Kwamishinan Ƴan sandan Jahar CP Lanre Bankole Wanda ya gabatar da masu laifin a hedikwatar rundunar dake Eleweran, Abeokuta, yace an kama masu laifin a faɗin jahar.
Kwamishinan ya kuma gabatar da wasu matasa wanda ake zargin sun kashe wani matashi, tare da tafiya da mashin ɗin a Ogere.
KARANTA WANNAN LABARIN: DA DAKON RAKE NAYI AURE, NA GINA GIDA, KUMA NAKE BIYAWA KANINA KUDIN MAKARANTA
Bankole ya kuma gabatar da Muhammad Abubakar ɗan shekara 42, da Clinton Niche ɗan Shekara 18, wanda suka kashe wani yaro mai shekaru 7 a Agbara ta Ado, ƙaramar hukumar Ado Ota ta Jahar.
Yace an kama masu laifin a lokacin da suke ƙoƙarin karɓar kuɗaɗen fansa daga iyayen yaran.
CP ya shaidawa manema labaru cewa rundunar a shirye take na magance ta’addanci da masu aikata shi a Jahar.
Yace “ina so in sanar da al’ummar jahar kula da lafiyar su a kowane lokaci, kuma zamu magance ta’addanci da masu aikata ta’addanci a ƙasar.
Ina kira ga al’ummar jahar dasu baiwa rundunar goyon baya ta hanyar bayar da bayanai masu amfani da zasu taimaka gami da haɗa hannu domin magance ta’addanci, kasancewar jahar na ɗaya daga cikin masu zaman lafiya a Ƙasar.
Kwamishinan ya kuma yi kira ga al’umma dasu tona asirin waɗanda suka lalata zaben shuwagabannin Jami’iyyar, wanda ɓangaren tsohon Gwamnan jahar Ibikunle Amosun ya gabatar da bindigar.