Rundunar Ƴan sandan Jihar Katsina ta samu nasarar ceto wasu mata guda huɗu da Yan Bindiga suka yi Garkuwa da su daga Karamar Hukumar Malumfashi.
Kakakin Rundunar SP Gambo Isah ne ya gabatar da matan ga Manema Labarai a Hedikwatar Rundunar da ke Katsina.
KARANTA WANNAN LABARIN:Abdullahi Abbas Ya Karbi Takardar Shugabanci Daga Uwar Jam’iyyar APC
Daga cikin matan su uku iyaye ne masu shayarwa wanda ƴan ta’addan suka yi garkuwa da su a Kauyen Garkar Karfi da ke Karamar Hukumar Malumfashi.
An samu nasarar ceto matan ne a dai-dai lokacinda Jami’an Ƴan sanda suka yi artabu da su a Karamar Hukumar Kankara a Karkashin Jagoranchin Baturen Yansanda na yankin.
Bugu da kari, an samu nasarar hallaka daya daga cikin yan ta’addan a lokacinda Ƴan sandan suka yi artabu da su a yayinda aka samu bindiga kirar AK 47 guda daya da harsasai.
Wannan ƙari ne bisa ga ƙwato Shanu 2 da tumaki 72 da Ƴann bindigar suka sato daga yankin.
An dai samu wannan nasarar ne a yayinda Ƴan sanda a ƘanƘara suka samu labarin afkuwar lamarin a Malumfashi inda suka toshe wata hanya da Ƴan bindigar suka biyo kuma suka cim masu.