Ƴan Sanda sun dakile wani Fashi da Makami a Niger
Ƴan sanda a jihar Neja sun ce sun dakile wani fashi da makami a hanyar Moroko a ƙaramar Hukumar Suleja ta jihar.
DSP Wasiu Abiodun, kakakin Rundunar Ƴan Sandan Jahar ya sanar da haka a Minna ranar Asabar.
Abiodun ya ce wasu da ake zargin ƴan fashi ne kusan su biyar ne suka kai hari a wani kantin sayar da wayoyi da wasu kayayyki da ke kan Hanyar Maroko, Suleja.
Sun yi harbe-harbe da bindiga tare da sace wasu wayoyin hannu a wani shago.
Ya ƙara da cewa, bayan samun bayanan ne jami’an ƴan sanda da ke yankin Suleja suka tunkari wajen da lamarin ya faru yayin da ƴan fashin suka yi gaggawar tafiya a cikin mota kirar Peugeot 406 tare da Reg.
Lambar motar ABJ467 GX, Abiodun ya ce, bayan wani zazzafan fafatawa da sojoji suka yi a shingen binciken ababan hawa da Zuma rock, ‘yan fashin suka yi watsi da motar suka shiga dajin.
Sai dai kuma jami’an ƴan sanda da sojoji na kan bin sawun ‘yan fashin da suka tsere da nufin kamo ‘yan ta’addan.
Kwamishinan ‘yan sanda, Monday Bala Kuryas, ya yi kira ga jama’a da kada su firgita saboda jami’an tsaro na kan gaba kan lamarin inda za’a bayyana wa jama’a abinda ke faruwa.
Kuryas ya nemi ƙarin goyon baya daga mazauna wurin ta hanyar fito da ingantattun bayanai game da abubuwan da ake zargi don ɗaukar matakan tsaro cikin gaggawa.