Rundunar ta kuma gabatar da wasu masu laifuka daban daban gaban yan jarida
Rundunar Yan Sanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar hallaka yan ta’adda guda 5 a karamar hukumar Musawa, a yayinda suka kai hari a wasu kauyuka biyu da suka shafi Kananan Hukumomin Matazu da Musawa.
Kakakin Rundunar SP Gambo Isah ne ya tabbatar da hakan a lokacinda yake gabatar da masu laifuka daban-daban da rundunar ta samu nasarar chafkewa.
Kamar yadda ya bayyana, an hallaka yan ta’addan ne a lokacinyda Area Commander na shiyyar Dutsin-ma ya jagoranchi jami’an shi bayan da aka samu rohoton sirri akan chewa yan ta’addan sun kai farmaki wasu kauyuka biyu.
KARANTA WANNAN LABARIN: AFCON 2021: An sanyawa wani filin wasa sunan Sadio Mane
Haka zalika kakakin rundunar ya ce sun samu nasarar kwace bindiga kirar AK 47 guda daya da harsasai guda 7 da dai sauran kayayyaki a wurin barayin.
Haka zalika, rundunar yansandan ta samu nasarar chafke masu laifuka daban-daban da suka hada da wadanda ake zargi da garkuwa da mutane da satar motoci gami da masu satar wayar fitilun hanya wato armoured cables da dai sauransu.
A wani labarin mai kama da wannan, rundunar ‘yan sandan jihar ta Katsina ta tabbatar da kama wani mai suna Abubakar Abdulbasir dan shekara 18 da ke zaune a garin Marabar Kankara da ke karamar hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina.
Gombo Isah ya kara da cewa wani mutun mai suna Sunusi Abubakar ne ya kai rahoto a caji ofis din ‘yan sanda cewa diyarsa yar shekaru 4 mai suna Halimatu Abubakar ta yi batan dabo.
A cewarsa sai mutumin ya ce daga baya aka kirashi da waya ana gaya masa cewa an yi garkuwa da diyarsa ana neman kudi naira dubu 70,000 ko Kuma ta rasa rayuwarta.
“Da jin wannan labarin sai jami’an’yan sanda na bangaran yaki da masu garkuwa da mutane suka fara aikinsu wanda daga karshe suka yi nasarar damke wanda ake zargi da aikata wannan baban aikabai’i Abubakar Abdulbasir.” Inji shi
Kakakin rundunar SP Gambo Isah ya ce a lokacin da jami’an tsaro suke gudanar da binciken wanda ake zargi ya amsa laifinsa, inda ya ce shi ya dauke ta ya ajiyeta acikin wani kangon gida a garin Marabar Kankara da ke cikin karamar hukumar Malumfashi.
Tuni dai aka kubutar da wanann karamar yarinya aka hada ta da iyayenta, ba tare da ta samu wani rauni ba ko cutarwa.
Daga karshe SP Gambo Isah ya bayyana cewa da zaran sun kammala bincike za su tura keyar wanda ake zargi zuwa gaban kuliya bantam sabo domin daukar matakin shari’a akan sa.
SP Gambo Isah yayi amfani da damar wurin mika sakon ta’aziyyar Rundunar ga Iyalan Baturen Yan Sanda Na Jibia da Yan Ta’adda Suka Hallaka kananan.