Ƴan Sanda sun hallaka Direban Mota da Yaron sa a Ogun
Da yawa daga cikin Matafiyan dake tafiya akan hanyar Abeokuta-Papa-Sango-Lagos sun Cirko-Cirko a yayinda wasu Jami’an Ƴan Sanda na Jahar Ogun suka harbe Direba da yaron motar sa.
Lamarin ya faru ne a yankin Itori na kan Babbar Hanyar Lagos-Abeokuta.
KARANTA WANNAN LABARIN: NSCDC ta horas da Jami’an ta kan bunƙasa zaman lafiya da Sasanta Rikici a Katsina
Wakilin Majiyar mu ya gano cewa Ƴan Sandan a cikin motar su ta kai samame sun ga Wanda Suka hallaka yana tuƙi akan hanyar su domin su kauce wa inda bashi da kyau na hanyar a Ƙaramar Hukumar Ewekoro, wannan laifin dai tuni sun amsa shi kamar yadda ƴan sandan suka buƙata.
Wani wanda ya shaida lamarin yace “a lokacin da suka hangi motar Ba zuwa sun gaya mashi yayi baya. Sai yaƙi yin baya, sai suka harbi tayar motar sa.
“Wannan ne ya haddasa hayaniya tsakanin su, sai wani Ɗan Sanda kawai ya harbe Direba da yaron sa.
“Wannan ne ya sanya matasan garin Itori suka rufe hanyar domin yin zanga-zangar akan wannan kisa na rashin adalci ga ƴan sandan
A lokacin da aka tuntuɓe shi, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar Ƴan Sandan Jahar Ogun Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da faruwar lamarin, amma yace har yanzu baida gamsashshen bayani akan lamarin