Ƴan sanda sun kama Ɗan damfara da yake sajewa a Matsayin Matafiyi a Legas
Rundunar Ƴan sanda a Legas ta kama wani mutum mai suna Emmanuel Rowland mai shekaru 34 bisa zargin sa da aikata zamba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hisbah ta ƙwace kwalaben barasa 384 a Jigawa
Jami’an ƴan sanda reshen Ipakodo na Jihar suka kama wanda ake zargin.
Jami’in Hulda da Jama’a, SP Benjamin Hundeyin, ya ce an kai Rowland ne a gidan yari bayan da aka kawo koken sa kan aikata laifin.
wanda ake zargin tare da wasu ana zargin su da damfarar Matafiya sa suka shiga Motar su.
“Wanda ake zargin, tare da wasu, yayin da suke aiki a cikin wata mota kirar Volkswagen Jetta Saloon, mai lamba JJJ 27 DG, Suna nuna kansu a matsayin direba da fasinjoji.
“Sun dauki fasinjojin tare da fara tattaunawa game da wasu kuɗaɗe da ake zargin an ajiye a cikin takalmin motar su.”
Rwoland ya amsa cewa ya fara aikata laifin ne a watan Janairun 2022 kuma an kama shi ne lokacin da yaje fita ta shida domin aikata laifin.
PRO ya kara da cewa ana ci gaba da farautar ƴan kungiyar da suka gudu da sauran masu aikata laifi irin wannan.
Kwamishinan Ƴan Sanda, Abiodun Alabi ya bayar da umarnin a ci gaba da bincike kan lamarin kafin a gurfanar da shi gaban ƙuliya.