Ƴan Sanda sun Kama Manyan Masu Laifi 42 a Adamawa
Shiyya ta 3 ta Rundunar Ƴan Sanda mai kula da Jihohin Adamawa, Taraba ya kama manyan masu laifi guda 42 daga maɓoyar su a Jahar Adamawa.
Waɗanda ake zargin, sun kasance masu kananan Shekaru ne a Adamawa da akafi sani da Shila Boys, an kama su ne da kayayyakin da suke amfani dasu wajen ɓalle gidajen mutane, da kuma ƙwayu da suka haɗa da Tiramol, Tabar Wiwi, kayan ruwa da aka fi sani da Suck and Die, da sauran su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ku sanya buƙatar kafa Ma’aikatar Dabbobi, wasu buƙatu namu, ko ku rasa ƙuri’un mu – Fulani Ga Ƴan Takara
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar na Shiyya 3 SP Yusuf Adamu ya bayyana haka a cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Litinin, ya bayyana cewar kamo su ya biyo bayan umarni da Mataimakin Sufeto-Janar na Shiyyar AIG Daniel Sokari Pedro.
Adamu yace tunda farko ya umarci Mataimakin Kwamishina mai kula da kai samame a Jahar Adamawa daya kawo ƙarshen Shila Boys da sauran ƴan ta’adda a Shiyyar.
“Jami’an ƴan sanda sun yi saurin zuwa wurin su, tare da kamo mutane 42 da suke da hannu akan laifin”, Inji Sanarwar.
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Shiyyar yace kamen daya sanya aka kama mutane 42 daga ƴan sandan Shiyyar na daga cikin kokari da Jahohin suke yi a karkashin Shiyyar.