Rundunar Ƴan Sandan Jahar Katsina tace ta samu nasarar kama biyu daga cikin waɗanda ake zargin sun kashe Ɗan Shekara 30 Umar Abdullahi Ankalele na Ƙaramar Hukumar Faskari ta Jahar Katsina.
Marigayi Ankalele, kamar yadda rahoton Ƴan Sanda ya bayyana, sun kai mashi hari ne a ranar 1 ga watan Maris na Shekarar 2022 a gidan sa dake Dogon Awo na Ƙaramar Hukumar Faskari, wanda Ƴan ta’adda guda bakwai suka yi.
Ankalele, wanda aka bayyana cewa yaƙi bin su zuwa Daji, ƴan bindigar sun kashe shi, inji Ƴan Sanda.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ba mu fara karɓar kuɗaɗen Hajji bana ba — Hukumar Alhazai ta Kano
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan SP Gambo Isah ya bayyana haka a ranar Talata, a lokacin da yake gabatar waɗanda ake zargin guda biyu da suke da hannu da Kisan ga Manema Labaru.
Sunayen su kamar yadda SP Gambo Isah ya bayyana a lokacin da yake gabatar dasu, sun ƙunshi Nasiru Mohammed mai Shekaru 27, da Abubakar Iliyasu Dan Shekara 25, dukkanin su daga Ƙaramar Hukumar Faskari.
A lokacin bincike, dukkanin su sun amince da aikata laifin, suna masu cewa basu kaɗai bane. Sai suka bada sunayen wasu da suka haɗa da Yellow, Samaila, da Ibrahim, da Sani dukkanin su ƴan Asalin garin Yankara, da garin Dajin Ƴar-Malamai ta Ƙaramar Hukumar Faskari.
A lokacin da suke amsa laifin, Abubakar Iliyasu yace “Yellow shine ya jagorance su zuwa kai harin. Shine ya jagorance mu zuwa gidan Ankalele domin sace shi, amma a lokacin da yaƙi bin mu, ɗaya daga cikin mambobin mu Abdullahi Iliya ya harbe shi ta hanyar amfani da AK 47.
“Shugaban mu baiji daɗi ba daya kashe Ankalele, shima sai ya kashe Abdullahi Iliya (wanda ya kashe Ankalele) a dalilin abinda ya yi.
Abubakar Iliyasu ya bayyana cewa Abdullahi Iliya (Makashin Ankalele) ɗan uwansa ne na jini, kuma dukkanin su, suna gudanar da ayyukan ta’addanci a tare a yankunan su.