Rundunar Ƴan Sandan Jahar Kaduna ta kama wani jami’in Hukumar Kula da Ƙa’idojin Titi ta Jahar Kaduna, wanda aka yi zargin ya kashe wani mai mota har lahira akan hanyar Ali Akilu dake Unguwar Sarki a cikin birnin Kano a ranar Juma’a.
Kama shi ya biyo bayan umarnin da Kwamishinan Ƴan sanda na Jahar Mudassiru Abdullahi ya bayar, kamar yadda Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar ASP Muhammad Jalige ya bayanna.
KARANTA WANNAN LABARIN: An farmaki wani ƙaramin barikin Soji, anyi awon gaba da Motocin sintirin su
Lamarin kamar yadda shaidu gani da ido suka bayyana ya faru ne da misalin ƙarfe 4 na rana, wanda ya haifar da rikici a Unguwan Sarki ta Jahar.
An kuma gano cewa direban an kashe shi ne biyo bayan maganganu tsakanin sa da Jami’in Hanya.
Shaidun sunce Direban ya rasu bayan jikkata a kansa, bayan ya bugu da sanda, sakamakon maida magana.
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar a lokacin da yake tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewar Kwamishinan Ƴan sanda ya bada umarni a kama jami’in hanyar dake bayan wannan aika-aika.
Jalige yace tuni Rundunar ta fara bincike akan lamarin domin gano abinda ya faru.