Jami’an Hukumar Jami’an tsaron Sibil Difens a ranar Talata sun ci zarafin ƴan jarida tare da Dukan Wakilin Jaridar The Nation Mr Toba Adedeji a lokacin da yake daukar rahoto akan zanga-zangar Ɗalibai a hedikwatar NSCDC dai Osogbo, Babban Birnin Jahar.
Wani daga cikin zaƙaƙƙen Jami’in Tsaron Sibil Difens ya tunkari Adedeji a gurin, tare da tuhumar shi, duk cewa dan jaridar ya nuna masa kan sa a matsayin Wakilin Jaridar The Nation.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Jihar Ogun Ta Yi Allah-wadai Da Karuwar Fyade, Laifukan GBV
Wannan bai hana Jami’an tsaron NSCDC daga dukan sa ba, inda suka ce Adedeji ya gaigayawa Babban su magana. Jami’an tsaron ya samu taimakon abokanan aikin sa wajen cin zarafin ƴan jarida.
A yayinda wasu ƴan jarida suka yi ƙoƙarin ceto Adedeji daga Jami’an tsaron Sibil Difens, wani daga cikin jami’an yayi barazanar harbin sa tare da cin mutuncin su.
Adedeji ya bayyana kamar haka “ina tsaye a ƙarƙashin inuwar shiga hedikwatar NSCDC ina aiki da waya ta, a yayinda zanga-zangar ke cigaba da wakana. Wani ya ƙalubalance ni da ɗan leƙen Asirin ƴan sanda.
“Na gaya mashi cewa Ni ba ɗan leƙen Asirin ƴan sanda bane, wani ya bada umarnin a karɓi waya ta, zan nuna masu shaida ta da yake a ƙirjina, sai dai naji wani ya doke Ni, yana ƙoƙarin karɓar waya ta, sai wasu suka bi bayan sa wajen duka na.”
“Agogo na dake a hannun haguna an lalata mani shi a lokacin duka na. Sai daga baya abokanan aikina suka ƙwace ce, sun yi barazanar harbin wani daga cikin su.