Ƴan Ta’adda ɗaya daga cikin Matafiyan Abuja-Kaduna a hannun su
Mohammed Al’amin ɗaya daga cikin mutane 50 da aka sace a Jirgin Saman Abuja-Kaduna, ƴan bindiga sun Harbe shi inji rahoton Jaridar The PUNCH.
Ƴan bindiga a cikin makonni biyu da suka gabata sun saki mutane 11 daga cikin mutane 61 da aka sace bayan watanni 3 a magarƙamar su, a yayinda mutane 50 suka rage a wurin su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tikitin Gasar Cin Kofin Duniya Na ƙarshe Za A Fara Siyarwa A Mako Mai Zuwa – FIFA
Malam Tukur Mamu daga cikin wanda suke sasantawa da ƴan bindiga da kuma Sheikh Ahmad Gumi wanda ya bayyana haka, yace akan samun bayanai masu inganci a gare shi, lamarin ya faru ne a ranar Litinin.
A cewar Mamu, lamarin ya faru ne biyo bayan musayar wuta a Daji a tsakanin Ƴan bindiga dake tsaron su tare da hana su tserewa.”
Duk da yace sun raunata matafiyan amma har yanzu yana raye amma yana buƙatar kulawar lafiya.
Mamu, a cikin wata Jarida daya fitar da bayanai Desert Herald, yace Harbe ɗaya daga cikin Matafiyan zai iya zama da Son rai nasu, domin aike wani saƙo.
Yace ya roki ƴan bindiga dasu sake wanda suka harba, domin bashi kulawar lafiya, amma sun hana.
Ya bayyana cewa dole Gwamnatin Tarayya ta shirya amsar laifin kasa ceto sauran mutane 50 kafin su ida kashe su.
Ya bayyana damuwar sa na yadda yaita tattaunawa da Sasanci, amma Gwamnati taƙi ɗaukar wani mataki, yana cewa dole Gwamnati ta ɗauki aiki domin ceto su