Ƴan ta’adda a ranar Litinin sun kai hari a ƙauyukan Amaokwe da Okoko, dake al’ummar Item ta ƙaramar hukumar Bende ta jahar Abia, inda sukaita harbe-harbe a saman iska.
Duk da basu kashe kowa ba, amma sun ƙone motoci, da gidaje da sauran kayayyaki masu daraja.
Wani ya shaidawa majiyar jaridar Dimokuraɗiyyar cewa, ɓata garin sun zone domin ƙaƙaba dokar zaman gida a madadin ƙungiyar tsagerun IPOB, inda suka je a tsakiyar kasuwar Eke-Nta dake Okoko Item, tare da harbe-harbe ba tare da dalili ba, lamarin da ya haifar da tashin hankali a tsakanin mazauna yankin, wanda suka ruga domin tsira da rayuwar su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamna Ganduje Yace Kano Ta Shirya Tsaf Don Gudanar Da Babban Toron APC
Haka zalika, ba’a bayar da bayanai cewa kai harin nada nasaba da sanya dokar zaman gida, wadda tuni ƙungiyar IPOB ta dakatar.
Wakilin majiyar jaridar Dimokuraɗiyyar ya ruwaito cewar, mazauna yankin wanda suka tattaru domin gudanar da harkokin kasuwancin su, an sanya dole suka kulle shagunan su.
Mai magana da yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Geoffrey Ogbonna, ba’a samu damar magana dashi ba, domin dukkanin wayoyin sa da aka kira sun nuna baza’a iya samun sa ba.
Comments 1