Tsohon Sanata Mai Wakiltar Kaduna ta tsakiya Shehu Sani yace ya tsallake harin ƴan ta’adda, a lokacin da yake cikin jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna.
Sani ya bayyana haka a cikin wani jawabi daya fitar a ranar Alhamis, inda yace abun yasha mamaki na yanda shi da wasu matafiya suka tsere daga jirgin ƙasar.
Ya kuma bayyana cewa, ƴan ta’adda sun farmaki jirgin ƙasar a ranar Laraba a hare-hare da suka ƙaddamar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu masu Safarar ƙwayoyi sai sun tuntuɓi bokaye sun basu sa’a kafin su fara aikin su — Cewar Marwa
Sani yace “jiya ƴan ta’adda sun farmaki jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna da bama-bamai, da kuma buɗe wuta ga jirgin, inda suka hari Direban da kuma tankin man jirgin.
“Da safe kuma ina cikin jirgin ƙasa a sa’ilinda suka lalata jirgin, abun ya bamu mamaki na yanda muka tsere.
Haka zalika, har yanzu babu wani rahoto da yayi dai-dai da rubutun tsohon Sanatan wanda yayi akan lamarin daya faru a ranar Laraba.
A wani rubutu da wani Garba Muhammad yayi wanda yace yana cikin jirgin, yace jirgin ya samu matsala ne, wanda hakan ya sanya matafiya suka tsaya jira, na tsawon awanni shida.
“Yanzu ƙarfe ɗaya 1:46 wani jirgi da zaije Rigasa, bayan mun shafe awanni shida daga Abuja zuwa Kaduna, ya samu matsala, yanzu akwai sauran kimanin kilomita 40 zuwa Kaduna.
“Duk wanda ke cikin jirgin dole ya fuskanci wahala, da gajiya, da yunwa,” cewar Muhammad.