Sama da dalibai dubu 20 da suka rubuta jarabawar kammala sakandare ta Arabiya da na fasaha a Kanon Nijeriya, NBAIS na kokawa kan rashin sanin makomar ci gaba da karatunsu sakamakon gazawar gwamnatin Kano na biyan hukumomin NBAIS da NABTEB kudaden su.
Rahotanni sun nuna cewa gazawar gwamnatin Kano wajen rashin biyan kudaden ya jaza hukumomin jarabawar kammala Sakandare ta NBAIS da NABTEB suka ki sakin sakamakon jarabawar daliban na Kano, wanda hakan ya jefa daliban cikin fargaba rashin sanin makomarsu. Tare da rashin sanin samun dama a makarantun gaba da Sakandare.