Ƙungiyar Ɗalibai ta Najeriya tayi barazanar ɗaukar wani mataki akan Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i akan rashin cimma matsaya daya haddasa Ƙungiyar ASUU ta shiga yajin aiki.
NANS a Jawabin data fitar a ranar Litinin daga Shugaban ta Asefon Sunday Adedayo yayi gargaɗin tsunduma zanga-zanga a faɗin kasar domin tilasta wa Malamai su shiga aji.
ASUU dai ta sanar da shiga yajin aiki na watanni 4 wanda ya fara daga ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu na shekarar 2022, domin bayyana gazawar Gwamnati na cika alƙawurran data ɗauka da Ƙungiyar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hadiza Usman ta ci Taliyar Karshe, Yayin da Buhari ya Tabbatar da nada Bello-Koko Shugaban NPA
Shugaban Ƙungiyar ASUU Farfesa Emmanuel Osodeke a Jawabin Manema labaru a Lagos, yace Ƙungiyar taso ta hana faruwar yajin aikin amma Gwamnati bata damu da abubuwan da suke buƙata ba.
Osodeke yace tilasta wa mambobin ASUU biyan Albashi ta hanyar shigar dasu tsarin IPPIS, da rashin amfani da tsarin biyan Albashi na UTAS yana cigaba kawo canje-canje a mambobin Ƙungiyar.
Ƙungiyar Ɗalibai ta ɗora alhakin ha Gwamnati da ASUU akan shiga yajin aikin, yace ƙungiyar ɗaliban ta ɗauka zasu cimma matsaya tare da dukkanin abinda zasu iya domin hana faruwar yajin aikin.
Yace “Gwamnati da ASUU ta hanyar ɗaukar wannan matsaya, sun aika saƙo gaggarumi ga Ɗaliban Najeriya dasu dauki mataki.
Ya ƙara dacewa matakin ƙungiyar Ɗalibai zata sanar dashi a taron ta na ranar 17 ga watan Fabrairu .