Wasu Ɗalibai a Jami’ar Jos sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i dasu samar da wasu hanya domin magance yawaitar shiga yajin aiki a Jami’o’i.
Sun yi wannan kiran a tattaunawar su da Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa a ranar Juma’a a Jos.
KARANTA WANNAN LABARIN:Yanzu-yanzu: Najeriya, Kasashen Afirka Biyar Za Su Fara Samar Da Rigakafin Allurar COVID-19 – WHO
NAN ta bada rahoton cewa ASUU a ranar Litinin data gabata, ta ayyana shiga yajin aiki na wata ɗaya na gargaɗi domin neman a cika mata buƙatun ta, bayan ta dakatar da yajin aikin ta watanni 9 a watan Disamba na shekarar data gabata.
ASUU ta bayyana cewar Gwamnatin Tarayya har yanzu taƙi girmama buƙatun su da aka cimmawa tun shekarar 2009.
Ɗaliban sun yi kira ga ɓangarorin guda biyu dasu dawo tattaunawa, domin samo hanyoyin da za’a magance matsalar.
Miss Edlyn Pam Ɗalibai ƴar aji 4 dake Karantar ɓangaren Jarida a Jami’ar ta koka akan yawaitar yajin aikin wanda ya dawo da ɓangaren ilmi koma baya musamman a gare ta.
Wani Ɗalibin Kwaptoe Fred yace dukka da ASUU da Gwamnatin Tarayya ya kamata su maida hankali ƙwarai ga cigaban Ɗalibai.