Ƙungiyar Ɗalibai ta Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Ƴan Arewa, tayi barazanar kulle garin Zaria a Jahar Kaduna, sakamakon sace Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi 13.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya tace an sace su ne a lokacin da suka dawo daga ziyarar ta’aziyya.
An dai bada rahoton cewa an sace su ne Kidandan ta Ƙaramar Hukumar Giwa dake Jahar Kaduna a ranar Litinin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Masu garkuwa da Mutane sun hallaka wani Kaftin na Soja
Wata majiya ta tsaro ta nuna cewa Umar Abubakar (Katako) direban mota mai kujeru 18, daya ɗauko su, sun sako shi.
Sun umarce shi daya tafi, tare da sanar da ƴan uwan wanda lamarin ya shafa cewa sun sace Ma’aikatan.
Yace a rahoton gani da ido, ƴan bindiga guda 6, da bindiga ƙirar AK-47 sun tsayar da motar tare da sace mutanen ciki, mintuna 45 bayan ta bar ƙauyen Kaya.
Ya ƙara dacewa, bayan sunyi bincike tare da tafiya da kayayyakin matafiyan, sun tafi dasu cikin daji