Gwamnatin jihar Kano ta ce ta bada umarnin a ƙarawa ɗaliban jihar Kano alawus da ta ke biyan su, kasancewar wanda a ke basu a yanzu ya yi musu kadan.
Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan a ranar Asabar lokacin da ya halarci taron da ma’aikatar matasa da wasanni ta jiha ta shirya a wani ɓangare na bikin ranar matasa da majalisar ɗinkin duniya ta shirya.
Gwamna Ganduje ya ce, ƙudirin da majalisar Ɗinkin duniya ta yi na cewa a rinƙa sanya matasa a al’amuran ci gaba na duniya tuni jihar Kano ta yi nisa a wannan ɓangaren.
Har wa yau, da yake jawabi a yayin da ya ziyarci duba aikin gyare-gyare da a ke yi a hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa, Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya buƙaci shugaban hukumar Muhuyi Magaji Rimin Gadon da ya ci gaba da gudanar da aikin yaƙi da cin hanci da rashawa yadda ya kamata ba tare da ɗagawa dukkan wanda a ka samu da cin hanci da rashawa ƙafa ba.