Ɗan Acaɓa ya mutu a hannun Ƴan Sanda a Ogun bayan yasha Azabtarwa a hannun su
Wani Mai Shekaru 39 mai hayar babu Abiodun Oladede tuni rahoto ya karaɗe na yadda Ƴan Sanda suka riƙa dukan shi har ya mutu a lokacin da yake cikin Magarƙamar su a Jahar Ogun.
An dai kama shi a ranar 1 ga watan Afrilu wanda Sashen Ƙwararru ta kama shi biyo bayan rikici daya ɓarke a Itori, Ƙaramar Hukumar Ewekoro ta Jahar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ku baiwa Mata Takarar Kujerun Mataimakin Gwamna — CSO tayi kira ga Jam’iyyun siyasa
Wasu matasa sun yi zanga-zanga aka kashe wani Mai Babur ɗin haya a wannan ranar da aka kama shi.
Lamarin ya faru a yayinda wani mai Fasa bayan da Jami’an Hukumar Kwastam suka kama shi, sun kashe shi akan hanya.
Wannan lamari shi ya haifar da rikici, a yayinda wasu Matasa suka fara ƙone-Ƙone.
Haka zalika, Matasan sun lalata wani Otel da ake zargi Jami’an sun ɓoye, tare da lalata Dukiyoyi, a yayinda suka ƙone ababen hawa, wanda ya shafi Babbar Hanyar Lagos-Abeokuta n tsawon awa guda.
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Ogun Abimbola Oyeyemi yace an kama mutane 13 da ake zargin suna da hannu a kai harin.
Haka zalika, Oladele yana daga cikin mutanen da aka kama, wanda aka bayyana a matsayin kamen masu laifi.
A cewar Olugbenga a yayin da Oladele yake a hannun ƴan sandan, sauran waɗanda aka kama tare dashi an sake su akan beli.
A cewar sa Oladele ya mutu a hannun ƴan sanda bayan yasha Azaba da musguna wa a hannun ƴan sanda.
A lokacin da aka tuntuɓi Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Oyeyemi yace “ban da tabbaci cewa irin wannan lamarin ya faru. Amma zan gano, kuma zan yi maka magana.
Comments 1