Ɗan Majalisa mai wakiltar Jere a Majalisar Wakilai ta Jahar Borno Ahmed Satomi ya nisanta kanshi da cin zarafin wata yarinya mai suna Fadila Abdulrahman a Maiduguri.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewar Fadila Abdulrahman wasu magoya bayan ɗan siyasa suka farmake ta, a wajen saida abincin ta a Shehu Sanda Kyarimi.
Fadila dai ta zagi ɗan siyasar a shafin ta na Facebook a Maiduguri a kwanakin baya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-duminsa: An Gurfanar Da Wanda Ya Kashe Hanifa A Gaban Kotu
A cikin wata sanarwa daya fitar a Facebook a ranar Litinin, Satomi yace babu sanya hannun shi a cin mutuncin da aka yiwa Fadila. Yace ba baida masaniya akan mutanen da suka farmake ta da Fadila.
A cikin sanarwar tace “Ni Ahmed Satomi, Ɗan Majalisa mai wakiltar Jere a Majalisar Wakilai a Jahar Borno, ya bayyana rashin jindaɗin sa akan abinda aka yiwa Fadila Abdulrahman a ranar Lahadi a ranar 22 ga watan Janairun a Shehu Sanda Kyarimi a Maiduguri
“Banji daɗi da abinda ya faru musamman ga mace, abun baƙin ciki shine ya faru da suna na.
“Ina jajanta ma Fadila akan abinda ya faru da’ita da al’umma baki ɗaya, a yayinda zamu sanya ayi mata adalci,” inji Satomi.