Ɗan Majalisa Mai Wakiltar Mazaɓar Kwankwaso, da wasu mutum 3 sun ƙyale NNPP, sun koma APC
Ɗan Majalisa Mai Wakiltar Ƙaramar Hukumar Madobi, Mazaɓar garin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, Hon. Kabiru Yusuf Isma’il ya canja sheƙa daga Jam’iyyar NNPP zuwa Jam’iyyar APC Mai mulki a Jahar Kano.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnan Kogi ya naɗa Sabbin Manyan Sakatarori guda 10
Canja sheƙar sa yazo ne bayan kwanaki kaɗan da APC ta rasa Sanata Malam Ibrahim Shekarau wanda ya canja sheƙa zuwa NNPP, wanda Jagoran Jam’iyyar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya karɓa.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labaru Malam Muhammad Garba ya bayyana cewar Dan Majalisa Mai Wakiltar Ƙaramar Hukumar Kudu Mu’azzam El-Yakubu shima ya canja sheƙa daga NNPP zuwa APC.
Yace canje-canjen Jam’iyyar ya shiga NNPP musamman a tsakanin Ƴan Majalisun Jaha dana Tarayya.
Malam Garba yace Ɗan Majalisa Mai Wakiltar Ƙananan Hukumomin Bagwai/Shanono Isa Ali shima ya shigo Jam’iyyar bayan canja sheƙa daga APC zuwa NNPP.
Ana cigaba da samun canja Jam’iyya daga wannan Jam’iyya zuwa wata musamman a Jahar, a yayinda Babban Zaɓen Shekarar 2023 ke ƙaratowa.
A watan daya gabata, ƴan Majalisun Jaha 14 daga PDP da APC Suka koma NNPP, a yayinda wasu suka komo APC bayan kwanaki kaɗan da komawar su.
Comments 1