Ɗan Majalisa mai wakiltar Umuahia ta kudu a Jahar Abia Jerry Uzosike, ya koka akan yawaitar zaizayar ƙasa a Al’ummar Umunwanwa ta Ƙaramar Hukumar Umuahia ta Kudu a Jahar.
A cikin wata sanarwa daya aikewa Manema labaru, ya bayyana damuwar sa ga Al’ummomin yadda matsalar zaizayar ƙasa ta sanya wasu al’ummomin basa iya zuwa gidajensu da wuraren bauta.
Ɗan Majalisar ya kuma koka na yadda a dalilin matasalar zaizayar ƙasa, ya sanya sun rasa wutar lantarkin da suke amfani da’ita.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaɓen Shuwagabannin PDP: Yanzu mun shirya ceto Najeriya — Cewar Okowa
Ya kuma nuna rashin jindaɗi na yadda hukumomin gwamnati, da lamarin ya shafa har yanzu basu ɗauki wani mataki na magance matsalar ba.
Yace Majalisar Dokokin Jahar ta kuma rubuta wa Hukumar kula da jindaɗin yankin Niger Delta akan bukatar ta kawo ɗauki, amma har yanzu ba tayi komai domin magance matsalar ba.