Rundunar Ƴan Sandan Jahar Bayelsa tace wani Ma’aikacin ta, da ya tashi daga wajen aiki da ake kira da Sajan Akpoboloukeme ya daɓawa abokin aikin sa ɗan sanda wuƙa har lahira, sakamakon rashin fahimtar juna.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Juma’a daga bakin Mai Magana da Yawun Rundunar Asinim Butswat.
Butswat yace wanda lamarin ya faru a kanshi da ana kiran shi suna Sajan Sapele Eyerindeke.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ruftawar ginin Ikoyi: Iyalai zasu iya duba gawarwakin ƴan uwan su a yanzu — Gwamnatin Lagos
Acewar ta lamarin ya faru a ranar Alhamis, a yankin Edepie na Yenagoa Babbar Birnin Jahar.
Butswat yace jami’in na ƙoƙarin guduwa daga Bayelsa zuwa wata Jahar, bayan ya burmawa ɗan uwansa wuƙa kafin a kama shi.
“Lamarin ya faru a ranar 4 ga watan Nuwamba na shekarar 2021, da misalin ƙarfe 7 na Edepie na Yenagoa. An bada rahoton cewa Sajan Akpoboloukeme ya daɓawa abokin aikin sa Sajan Sapele Eyerindeke akan lamari ƙanƙane. Gawar marigayin an ajiye ta a Wurin ajiye gawa na Asibiti domin yin gwaji.
“Wanda ake zargin yayi gaggawar fita daga wurin daya aikata laifin zuwa wata Jahar, kafin a kama shi a ƙofar Glory Land Gate.”
Kwamishinan Ƴan Sandan CP Ben Okolo ya bada umarnin a tsare ɗan sandan.