Ɗan Shekara 18 ya mutu a Ruwa, a lokacin da yake Ƙoƙarin ceto Saniya a Jigawa
Wani yaro Ɗan Shekara 18 mai suna Adamu Musa ya mutu a kokarin ceto saniyar sa a karamar hukumar Buji ta jihar Jigawa.
KARANTA WANNAN LABARIN: ASUU ta kafa wani Kwamiti don yaƙi da labarun Ƙarya akan ta
Wani mazaunin garin ya shaidawa DAILY POST cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar a Unguwar Magina da ke cikin garin Buji.
Ya ce wanda abin ya shafa ya rasa ransa ne a wani tafki a lokacin da yake kokarin ceto saniyarsa da ta zame ta fada ciki a lokacin da take kiwo a kewayen yankin.
Kakakin Hukumar Kula da Tsaron Jama’a na NSCDC, CSC Adamu Shehu shi ma ya tabbatar wa DAILY POST faruwar lamarin.
A cewarsa, “Wannan mummunan lamari ya faru ne a ranar Asabar, 3 ga watan Satumba, 2022, da misalin karfe 02:00 na rana, inda matashin ya dauki shanunsa guda biyu zuwa gona, ya sako su domin ciyar da su da ciyawar da ke kusa.
“Abin takaici sai daya daga cikin shanun ta zame ta fada cikin wani tafki da ke kusa da gonar da suke kiwo.
“Da ya ga abin da ya yi muni, marigayin ya garzaya don ceto saniyarsa, amma ruwa ya nutse duk da kokarin da mutanen yankin da jami’an NSCDC suka yi na ceto shi,” inji shi.
Ya ce daga baya aka tsinci gawar mamacin ranar Lahadi da misalin karfe 01:00 na safe.
Ya ce an yi wa marigayin cikakken bincike, aka tabbatar da mutuwarsa sannan aka mika shi ga iyayensa domin su yi mashi jana’iza yadda ya kamata, yayin da aka ceto saniyar a raye.
A wani labarin kuma: Manyan ra’ayoyi ba sa cin zabe – Deji Adeyanju Ga Peter Obi
Wani mai sharhi kan harkokin siyasa, Deji Adeyanju, ya ce babu wani mai tunani da ra’ayoyi da zai lashe Zabe a nahiyar Afirka.
A cewar Adeyanju, ƴan takara masu karfi na siyasa ne kaɗai za su iya lashe zabe a Afirka.