Ɗan Shekaru 22 mai suna Aliyu Abdullahi dake Kasuwar Mata a Ƙaramar Hukumar Funtua ta Jahar Katsina, yan sanda sun kama shi da laifin da damfarar wata tsohuwa kuɗaɗen garatuti ta amfani da katin Karɓar kuɗi ATM, Kuma sai ya siyo Mota da Babur.
A cewar Jaridar Vanguard, matashin ya ƙware wajen cutar mutane ta hanyar canja masu katikan ATM nasu, an taɓa kamashi da wannan zaluncin tun bayan da ya samu ya fito da inda ake tsare dashi
Dayake maida jawabi akan yadda ya fita daga inda ake tsare dashi yace “lauyana ya karɓe ni beli bayan na shafe wata ɗaya a gidan yari.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Takarar Shugaban Kasa 2023: Tambuwal Ya Fara Tuntuban Jama’arsa
Ɗan Damfarar wanda ya sake dawowa a magarƙamar ƴan sanda ya tabbatar dacewa ya zalunci wata Maryam Sale dake Shararrar Pipes a cikin garin Katsina, inda ya cire mata kuɗaɗen garatuti nata, da kuɗaɗen data ajiye da yawan su yakai Naira miliyan 1,846,000.
Aliyu yace, “naje ATM domin in cire kuɗi a lokacin da tazo a Keke Napep, inda ta buƙaci in taimka in fito mata da dubu goma ta hanyar amfani da ATM. kafin cire kuɗin na duba asusun ajiyar ta, naga akwai kuɗaɗe masu yawa. Na cire mata kuɗin tare da canja mata katin ATM nata, bayan ta tafi sai naje wajen mai POS na cigaba da cire kuɗin. Na ɗauki kwanaki 3 kafin in cire duka ƙudin, inji shi.
A lokacin da aka tuhume shi akan inda kuɗaɗen suke yace ” na siyo mota Henesy Accord akan Naira dubu ɗari biyar da sabon Babur akan Naira 350,000, na kashe sauran wajen bushasha.