Ɗan Shekaru 76 ya nemi Kotu ta raba Auren su da Matarsa kan taƙi dafa abinci ga Ɗiyar su
Wani Ɗan Shekara 76 Mr. Samuel Akande a ranar Alhamis ya kai matar shi Gift ƙara Kotun Kwastamari dake Iyana-Ipaja kan taƙi dafa abinci ga ɗiyar shi data kawo masu ziyara.
Akande wanda yake zaune a Idimu na Lagos ya shaida wa Kotu cewa ya Auri matar shi shekaru 37 da suka gabata.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamna Ortom Ya Yi Allah-Wadai Da Rikicin Jukun Da Tiv, Ya Sha Alwashin Hukunta Masu Aikata Laifin
Ya kuma ƙalubalanci matar shi na yin fasiƙanci tare da hana shi haƙƙin Aure, da kuma cin mutunci.
“Mata ta bata sauraro na. Bata zama a gida. Tana tafiya coci. Kuma wani yazo gidana da hujja cewa yana kwantawa da mata ta.
“Matata ta ƙaryata hakan a lokacin da na tunkare ta, kuma abinda ya faru ɗiyar mu ta ziyarce daga Ibadan, amma taƙi dafa mata abinci,” inji shi.
Yace a lokacin da ya tambaye ta akan miyasa tayi haka, sai tace ɗiyar shi bata sanar da’ita cewa zata zo gidan ba, kuma Gift ta tabbatar cewa taƙi dafa abinci ga ɗiyar shi.
Kamfanin Dillancin Labaru ta ruwaito cewar abokin mijin Fasto Vincent Omojeye ya tabbatar da cewa matar taje wajen ɗiyar ta kuma bata haƙuri.
Bayan sauraron jin tabakin su, Mai Kula da Shari’a, Alƙaliya Mrs P.O. Adeyanju ya gargaɗi wadda ake ƙarar akan ɗabi’ar na ƙin tarbar ɗiyar su, tare da kira ga mijin daya baiwa matar dama ta biyu.