Mataimakin gwamnan jihar Katsina QS Mannir Yakubu ya bayyana cewa a shirye yake idan Allah ya ba wani nasara a zaben fidda gwani da Jami’yyar APC zata yi ba shi ya bishi domin samun nasara.
QS Mannir Yakubu ya faɗi haka a lokacin da yake ganawa ta musamman da ‘yan jarida a Katsina dangane da manufofinsa na jan ragamar jihar Katsina.
Haka kuma ya bayyana cewa acikin shekaru bakwai da ya yi a matsayin mataimakin gwamnan jihar Katsina ya taimaka wajan samun nasarar wannan gwamnati ta Aminu Bello Masari.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Har yanzu APC bata yanke shawarar inda zata bada Tikitin Tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa ba — Adamu
“Ni ɗan gwagwarmaya ne a siyasa saboda haka nasan cewa Allah shi ke bada mulki ga wanda ya so a lokacin da ya so, ina mai bada tabbacin idan ni Allah yaba alhamdullahi idan kuma wani ya ba zamu goya masa baya domin samun nasara baki ɗaya.” In ji shi
Da ya juya akan nasarorin da gwamnatin masari ta samu kuwa ya ce manoman jihar Katsina sune Alkalai akan irin cigaban da suka kawo ta fannin noma da bada iri da takin zamani acikin shekaru bakwai da suka yi akan karagar mulki.
QS Mannir Yakubu ya ƙara da cewa idan Allah ya bashi nasara zai ɗora akan ayyukan da gwamna Masari ya fara domin samun tabbataccen cigaban dimokuraɗiyyar a jihar Katsina.
” A ɓangaren ilimin kuwa wannan gwamnati ta yi rawar gani so sai musamman wajan gina sabbin makarantu da gyara wasu da samar da kujerun zama da ɗaukar ma’aikata fiye da dubu goma sha daya” inji shi
Kazalika ya yi tsokaci akan irin rawar da zai taka akan sha’anin tsaro idan ya samu nasara,inda zai tabbatar ya tsare rayukan al’umma da duniyoyin su.
Mataimakin na gwamnan Katsina ya yi bayanin cewa yana da sabbin tsare-tsare na inganta hanyar samun kuɗaɗen shiga wanda ya ce da su ne kowace gwamnati ke fita hakkin wadanda suka zaɓe ta
Comments 1