Ɗan takarar Jami’iyyar YPP a Shekarar 2021 a zaɓen Gwamnan Jahar Anambra Ifeanyi Uba ya kaɗa ƙuri’ar sa.
Mr Ubah ya kaɗa ƙuri’ar sa ne a Akwati mai lamba na 20 a Mazaɓar Otolo ta 1, a filin Nnofor ta Ƙaramar Hukumar Nnewi ta Kudu.
Dayake jawabi ga Manema labaru bayan ya kaɗa ƙuri’ar sa, Mr Ubah yace ya gamsu da fitowar masu kaɗa ƙuri’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴar Shekara mai buƙata ta musamman 70 tayi zaɓe, tace har yanzu bata karɓi garatutin taba
Yace akwai jinkiri na ƙarasowar kayayyakin zaɓe a Akwatin.
Ya kuma bayyana damuwa na jinkirin tantance masu zaɓe.
Wasu ƴan takara da suka haɗa da na Jam’iyyar PDP Valentine Ozigbo, da Sanata Andy Uba na Jam’iyyar APC, Suma sun kaɗa ƙuri’ar su.